Rebecca Kadaga | |||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
21 ga Yuni, 2021 - ← Moses Ali (en)
19 Mayu 2011 - 24 Mayu 2021 ← Edward Ssekandi (en) - Jacob Oulanyah (en) →
| |||||||||
Rayuwa | |||||||||
Haihuwa | Kamuli (en) , 24 Mayu 1956 (68 shekaru) | ||||||||
ƙasa | Uganda | ||||||||
Karatu | |||||||||
Makaranta |
Jami'ar Makerere Namasagali College (en) University of Zimbabwe (en) University of Zimbabwe Faculty of Law (en) | ||||||||
Harsuna |
Turanci Soga (en) | ||||||||
Sana'a | |||||||||
Sana'a | Lauya da ɗan siyasa | ||||||||
Imani | |||||||||
Jam'iyar siyasa | National Resistance Movement (en) |
Rebecca Alitwala Kadaga lauya ce kuma 'yar siyasa ce 'yar ƙasar Uganda wacce ta yi aiki a matsayin Kakakin Majalisar Uganda daga ranar 19 ga watan Mayu shekarar, 2011 har zuwa ranar 21 ga watan Mayu shekarar, 2021. A halin yanzu kuma tana aiki a matsayin mataimakiyar Firayim Minista na farko na Uganda. A lokaci guda kuma tana aiki a matsayin minista mai kula da al'ummomin yankin gabashin Afirka, a majalisar ministocin Uganda. Ita ce mace ta farko da aka zaɓa a matsayin shugabar majalisar a tarihin majalisar dokokin Uganda.Ta gaji Edward Ssekandi, wanda ya zama Kakakin Majalisa daga shekarar, 2001 zuwa shekarar 2011.
Ita ce kuma ƴar majalisa a yanzu (MP) mai wakiltar mazaɓar Kamuli ta mata ta yankin Busoga, wannan muƙamin tana riƙe dashi tun shekarar, 1989.[1][2]
© MMXXIII Rich X Search. We shall prevail. All rights reserved. Rich X Search